RA'AYI NA GAME DA KATOBARAR DA SHUGABAN KASA YAYI A GAME DA MATASA.
MATASAN NAJERIYA RAGWAYE NE MALALATA KUMA MARASA ILIMI.
Ni bazan fusata da wannan maganar ba, domin daga cikin malalatan matasan Najeriya ne danka Yusif yake hawa babban mashin mai matukar tsada dogaron sa kawai daga man fetur ne. Cikin kudin man fetur aka kaishi waje aka nema masa magani, cikin su ne kuma ak dauki hayar jirgin sama har aka dawo dashi gida.
Duk da haka ban fusataba dan ka kiramu malalata somin ga wadansu manyan malalatan marasa aikin yi suna ta kokarin karewa tare da canza maganganun batancin ka ga matasan Najeriya.
Taya zamuyi Ilimi? Bayan lokacin da kayi naka kayi FREE EDUCATION ne wato kyauta, yayin da a yanzu duk wani tallafi kun janye. Ilimi yayi bala'in tsada.
Baba lokacin kuruciyar ka ne fa ka rike mukamin Gwamna da Kwamishinan Man fetur sannan kuma ka zama Head of State, Yayinda Malalatan matasan yanzu bamu da wani aiki sai hawa Social media wasu na suka wasu na kareka.
Mai girma Shugaban kasa, nifa ban fusata tabbas mu matasan Najeriya ragwayene domin daga lokacin da kahau karagar mulki babu wani cigaba wajen daukar ma'aikata kuma ma ai dukkan jami'an gwabatin ka kashi 95% ba matasa bane duka Tsofaffi ne samfurin da.
Mai girma shugaban kasa, a kasar da kaje kazauna gaban manya shugabannin duniya har kake aibata matasan Najeriya, Shin bakasan irin tanajin da sukayi ma matasan kasarsu bane ba? Acan matasafa free education suke yi, lafiya ma free ne, kai hatta WiFi sun tanaje shi free wa matasa, har sukan bayar da rance wa matasa domin su fara kasuwancin su. Amma a kasar ka fa? Nasan dukan wadannan abubuwan da na lissafa Ragwayen matasan sune suke nema ma kansu da kansu.
Koda yake duk da kokarin da wadannan ragwayen matasan suke yi Akwai kadan daga matasan da suke fantamawa wadanda dogaron su na ga ribar manfetur, Baburan su, Motocin su, jiragen da ake daukar su akaisu yawon bude ido, hatta Manyan kwamfutocin su da wayoyin su dama DATA duka dogaron su daga man fetur ne.
To in banda rashin Aikin yi ma na matashin Najeriya, wa zaije filin jirgi ya wuni wai yana so yayima shugaban kasa barka da dawowa daga kasashen turai. Tirr!!!
Mu koma farko, Malalatan matasane suke bin bangwaye da wayoyin lantarki suna lika SAI BABA wai suna yima DANTAKARAR SHUGABAN KASA mara da zuwa garinsu Campaing.
Sune sukayita wasa ba ababen hawa wasuma har suna rasa rayukan su kawai dan BABA yacu zabe. Malalatan matasa ne suke tattaki daga garuruwan su zuwa Abuja Villa domin su taya BABA murnar cin zabe. Wasu a kekuna wadansu ma malalatan a kasa.
Kana iya fadin Albarkacin bakinka a akwatin Comments
ReplyDelete