Barka da zuwa DANDALIN ABUBAKAR A GWANKI, wannan sabon shafi ne amma har yanzu ana kan gina shi.
Popular posts from this blog
Fitattun Abubuwan mamaki guda bakwai a duniya
Akwai wadansu Abubuwa guda bakwai da duniya ta amince da su a matsayin sune abubuwan da suka fi ko wanne abin ban mamaki wanda dan'adam ne da kansa ya gina su. 1.Ginin Taj Mahal na Ƙasar Indiya 2.Ƙasaitacciyar katangar ƙasar Chaina, wandda aka fi sani da suna “Great Wall of China’’ a Tutance. 3.Mutum mutumin Yesu al-Masihu dake Ƙasar Brazil, Wanda aka fi sani da suna “Christ the Redeemer’’ a Turance. 4.Wani Birnin kan tsauni da ake kira (Machu-picchu) a Ƙasar Peru. 5.Sai kuma Birnin da ake kira da suna (Chichen Itza ) wanda aka gina a siffar dala a Ƙasar Mexico. 6.Gidan Tarihi na Petra da ke birnin Jordan. 7.Sai hamshaƙin Dakin Taro dake birnin Rum a Ƙasar Italiya, Wanda aka fi sani da “Colosseum’’ a Turance. Waɗanna dai sune abubuwa bakwai da aka yarda da cewa ɗan Adam ya nuna gwaninta wajen gina su a wannan Duniya tamu.
Abubakar A Gwanki Ya jagoranci taro kan yadda ake rubutu a Wikipedia
A ranar 20 ga Watan Maris na 2021, aka gudanar da wani muhimmin taro a ɗakin taro na ɓangaren ɗakin karatu na makarantar School For Arabic Studies a cikin birnin Kano. Taro ne wanda aka gudanar da shi domin ya koyar da mahalarta taron yadda ake rubutu a shafin Ilimi na Hausa Wikipedia. Taron wanda Wikimedia Foundation da kuma Hausa Wikimedians User Group suka ɗauki nauyin gudanarwa anyi shine ƙarƙashin jagoranci da kulawar Muhammad Mustapha Aliyu Shugaban Wikipedia sashen Hausa. Abubakar A Gwanki ne ya jagoranci taron inda yayi jawabai da dama ga mahalarta taron. Ga wasu hotuna daga taron Tare da Mustapha Gfatu, ƙwararre a fannin Na'ura mai ƙwaƙwalwa Bashir Sani Gwanki yana gabatar da jawabi Abubakar A Gwanki yana jawabi Abubakar A Gwanki yana jawabi Abubakar A Gwanki yana jawabi Mahalarta taron
Comments
Post a Comment