Fitattun Abubuwan mamaki guda bakwai a duniya
Akwai wadansu Abubuwa guda bakwai da duniya ta amince da su a matsayin sune abubuwan da suka fi ko wanne abin ban mamaki wanda dan'adam ne da kansa ya gina su. 1.Ginin Taj Mahal na Ƙasar Indiya 2.Ƙasaitacciyar katangar Æ™asar Chaina, wandda aka fi sani da suna “Great Wall of China’’ a Tutance. 3.Mutum mutumin Yesu al-Masihu dake Ƙasar Brazil, Wanda aka fi sani da suna “Christ the Redeemer’’ a Turance. 4.Wani Birnin kan tsauni da ake kira (Machu-picchu) a Ƙasar Peru. 5.Sai kuma Birnin da ake kira da suna (Chichen Itza ) wanda aka gina a siffar dala a Ƙasar Mexico. 6.Gidan Tarihi na Petra da ke birnin Jordan. 7.Sai hamshaÆ™in Dakin Taro dake birnin Rum a Ƙasar Italiya, Wanda aka fi sani da “Colosseum’’ a Turance. WaÉ—anna dai sune abubuwa bakwai da aka yarda da cewa É—an Adam ya nuna gwaninta wajen gina su a wannan Duniya tamu.