1. Najeriya ce kasa ta bakwai mafi yawan mutane a duniya, mai dauke da mutane sama da miliyan 200. Duk da cewa hakan na iya zama mutane da yawa, amma yawan mutane zai fi haka in ba don yawan mace-macen kasar da karancin shekarun rayuwa ba. 2. Duk da cewa akwai addinai mabambanta da ake yi a Najeriya, amma yawancin ƴan ƙasar Kirista ne ko musulmi. 3. Garin Igbo-Ora ne akafi yawan haifar Tagwaye. Da yawa daga cikin Yarbawa na yankin sun yi amannar cin naman daji da ganyen kuɓewa a matsayin dalilin haihuwar tagwayen da suke yi. Yayinda wasu masanan haihuwa suka yi amannar cewa wasu doya na dauke da kwayar halitta wacce zata iya haifar da yawan haihuwa, amma dai babu wata shaidar kimiyya game da wannan lamarin. 4. Najeriya kasa ce mai dimbin yawa tare da harsuna sama da 520. Yayinda Turanci ne yaren hukuma, Hausa, Yarbanci da Igbo suma manyan harsuna ne a kasar. 5. Lagos, tsohon babban birnin tarayyar Najeriya kafin a koma da shi zuwa Abuja, shi ne birni mafi girma da kuma yawan ja