Wasu abubuwa da ya kamata Ku sani game da Najeriya

 1. Najeriya ce kasa ta bakwai mafi yawan mutane a duniya, mai dauke da mutane sama da miliyan 200.  Duk da cewa hakan na iya zama mutane da yawa, amma yawan mutane zai fi haka in ba don yawan mace-macen kasar da karancin shekarun rayuwa ba.

2. Duk da cewa akwai addinai mabambanta da ake yi a Najeriya, amma yawancin ƴan ƙasar Kirista ne ko musulmi. 

3. Garin Igbo-Ora ne akafi yawan haifar Tagwaye.  Da yawa daga cikin Yarbawa na yankin sun yi amannar cin naman daji da ganyen kuɓewa a matsayin dalilin haihuwar tagwayen da suke yi.  Yayinda wasu masanan haihuwa suka yi amannar cewa wasu doya na dauke da kwayar halitta wacce zata iya haifar da yawan haihuwa, amma dai babu wata shaidar kimiyya game da wannan lamarin.


 4. Najeriya kasa ce mai dimbin yawa tare da harsuna sama da 520.  Yayinda Turanci ne yaren hukuma, Hausa, Yarbanci da Igbo suma manyan harsuna ne a kasar.


 5. Lagos, tsohon babban birnin tarayyar Najeriya kafin a koma da shi zuwa Abuja, shi ne birni mafi girma da kuma yawan jama'a a kasar.


 6. Masana’antar shirya fina-finai ta kasar, wacce aka fi sani da Nollywood, tana daya daga cikin manya-manyan furodusoshin fina-finai a duniya, sai na biyu a bayan Bollywood na Indiya.


 7. Najeriya gida ne ga Aliko Dangote, mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka.  Bukatun kasuwancin Dangote a fannin noma, banki, siminti, masana'antu, gishiri da sukari sun samu zunzurutun kuɗi sama da dala biliyan 12.


8. Najeriya itace kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka.  Yayin da masana'antar noma ke samar da kusan kashi 70 cikin 100 na aikin yi a kasar, kayayyakin man fetur su ne kayan da ake fitarwa na farko — wanda ya kai sama da kashi 90 na kayan da ake fitarwa daga Nijeriya.


 9. Kamar a wasu ƙasashen Afirka, mutanen Najeriya suna ɗaukar hannun hagu a matsayin ƙazanta kuma amfani da shi alama ce ta rashin ladabi.  Waɗanda suka yi imani da wannan ba sa cin abinci, girgiza hannu ko karɓar abubuwa da hannun hagu.


 10. Duk da samun ‘yancin kansu a shekarar 1960, amma Nijeriya ta kasance memba a kungiyar tarayyar Burtaniya, kungiyar kasashe 53 masu cikakken iko.  Kasar kuma memba ce ta Tarayyar Afirka.

Comments

Popular posts from this blog

Fitattun Abubuwan mamaki guda bakwai a duniya

Watari Dam