Skip to main content

Posts

Dandalin Abubakar A Gwanki

Shafin yanat gizo na Musamman mallakin Abubakar A Gwanki. Muna aiki akan shi har yanzu...
Recent posts

Fitattun Abubuwan mamaki guda bakwai a duniya

Akwai wadansu Abubuwa guda bakwai da duniya ta amince da su a matsayin sune abubuwan da suka fi ko wanne abin ban mamaki wanda dan'adam ne da kansa ya gina su.


1.Ginin Taj Mahal na Ƙasar Indiya


2.Ƙasaitacciyar katangar ƙasar Chaina, wandda aka fi sani da suna “Great Wall of China’’ a Tutance.


3.Mutum mutumin Yesu al-Masihu dake Ƙasar Brazil, Wanda aka fi sani da suna “Christ the Redeemer’’ a Turance.4.Wani Birnin kan tsauni da ake kira (Machu-picchu) a Ƙasar Peru.


5.Sai kuma Birnin da ake kira da suna (Chichen Itza ) wanda aka gina a siffar dala a Ƙasar Mexico.


6.Gidan Tarihi na Petra da ke birnin Jordan.
7.Sai hamshaƙin Dakin Taro dake birnin Rum a Ƙasar Italiya, Wanda aka fi sani da “Colosseum’’ a Turance.


Waɗanna dai sune abubuwa bakwai da aka yarda da cewa ɗan Adam ya nuna gwaninta wajen gina su a wannan Duniya tamu.

Kalli wakar رضيت بالله ربا daga ما هر زين

Wakar Maher Zain ta Raditu Billahi Rabba Wa bil Islami Deena. Kallo kyauta akan Youtube daga Abubakar A Gwanki.

Kai gaskiya wannan wakar tayi sosai, domin kuwa wakace da aka dorata akan doron imani da tauhidi zalla. Wannan ne ya kara sani son mawakai Maher Zain sosai.

Nahiyar Afrika

Africa Ko kum a hausance mukan ce Afrika , Itace Nahiya ta biyu mafi girma a Duniya bayan nahiyar Asiya, a wajen yawan Al'umma da kuma fadin kasa. Fadin kasar Nahiyar Afrika yakai miliyan 30.3kilomita daidai da (sukwayamil miliyan 11.7) Idan aka hada duka fadin nahiyar Afrika da tsuburran da suke kewaye da ita kashi 16% na na fadin duniya yana Afrika sannan Kaahi 20% na fadin kasar duniya yana Nahiyar Afrika ne. Ya zuwa kididdiga ta 2016 yawan kashi 16% na mutanen duniya yan Afrika ne, kimanin mutane biliyan 1.2. Nahiyar Afrika na da kasashe masu yancin kansu guda 54 Zamuci gaba da kawo maku bayanai a game da tarihin Nahiyar Afrika da kuma rabe-raben yankunan ta tare da zamantakewar al'umar nahiyar baki daya.

SASSAN DUNIYA

ASSALAMU ALAIKUM JAMA'A. DANDALIN ABUBAKAR A GWANKI Ya shirya tsaf domin kawo maku wani fili na musamman a cikin sa wanda akama lakabi da SASSAN DUNIYA wannan fili zai mayar da hankali ne wajen yima jama'a musamman ma hausawa bayani a game da sassan duniya da rabe raben su. Misali NAHIYA, me ake nufi da ita? Guda nawa ta rabu? Kaso-kaso na Nahiyoyi da harya zuwa kasashe da dai sauran su. Sannan wannan fili zai runka dan karkatawa har zuwa yanayin rayuwar mutane a nahiyar su da al'adun su. Abubakar A Gwanki Nine mamallakin wannan shafin kuma nine zan rinka kawo maku wadannan shirye-shiryen Insha Allahu.

Dandalin Abubakar A Gwanki

Assalamu Alaikum, kuna iya kasancewa dani a shafinFACEBOOKIdan kun latsa wannan. sannan kuma har yanu dai wannan shafi yana cikin yan gyararraki kuma da zarar komai ya kammala zaku fara jinmu sosai.dandalin Abubakar A Gwanki, domin ilimantarwa da nishadantarwa